Revelation of John 21

Sabuwar Urushalima

1Saʼan nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. 2Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. 3Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yǎ kuma zama Allahnsu. 4Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin alʼamura sun shuɗe.”

5Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.”

6Ya ce mini: “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai. 7Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana. 8Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata-wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutan da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”

9Ɗaya daga cikin malaʼikun nan bakwai masu kwanonin nan bakwai cike da annoban nan bakwai na ƙarshe, ya zo ya ce mini “Zo, zan nuna maka amaryar, matar Ɗan Ragon.” 10Ya kuwa ɗauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsayi, ya kuma nuna mini Birni Mai Tsarki, Urushalima, tana saukowa daga sama, daga Allah. 11Ya haskaka da ɗaukakar Allah, haskensa kuwa ya yi kamar luʼuluʼu mai daraja sosai, kamar jasfa, yana ƙyalƙyali kamar madubi. 12Yana da babbar katanga mai tsayi, mai ƙofofi goma sha biyu, da kuma malaʼiku goma sha biyu a ƙofofin. A bisa ƙofofin an rubuta sunayen kabilai goma sha biyu na Israʼila. 13Akwai ƙofofi uku a gabas, uku a arewa, uku a kudu, uku kuma a yamma. 14An gina katangar birnin a kan tushen gini goma sha biyu, a kansu kuwa akwai sunayen manzannin sha biyu na Ɗan Ragon.

15Malaʼikan da ya yi magana da ni yana da sandan awo na zinariya don awon birnin, ƙofofinsa, da kuma katangarsa. 16Birnin murabbaʼi ne, tsayinsa daidai ne da fāɗinsa. Ya auna birnin da sandarsa ya kuwa sami mil 1, 400 (wajen kilomita 2, 200) tsawonsa, fāɗinsa da kuma tsayinsa daidai suke. 17Ya auna katangarsa ya kuma sami ƙaurinta kamun 144, bisa ga maʼaunin mutum, wanda malaʼikan ya yi amfani da shi. 18An yi katangar da jasfa, birnin kuma da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi. 19Tushen ginin katangar birnin kuwa an yi masa adon da kowane irin dutse mai daraja. Tushe na farko an yi shi jasfa, na biyu saffaya, na uku agat, na huɗu zumurrudu, 20na biyar onis, na shida yakutu, na bakwai kirisolit, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofuras, na goma sha ɗaya jasin, na goma sha biyu kuma ametis. 21Ƙofofi goma sha biyun nan luʼuluʼai goma sha biyu ne, kowace ƙofa an yi ta da luʼuluʼu guda. Babban titin birnin kuwa an yi shi da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi.

22Ban ga haikali a cikin birnin ba, domin Ubangiji Allah Maɗaukaki da kuma Ɗan Ragon ne haikalin birnin. 23Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, gama ɗaukakar Allah tana ba shi haske, Ɗan Ragon kuwa shi ne fitilar birnin. 24Alʼummai za su yi tafiya cikin hasken birnin, sarakunan duniya kuma za su kawo darajarsu cikin birnin. 25Ba za a taɓa rufe ƙofofin birnin da rana ba, gama ba za a yi dare a can ba. 26Za a kawo ɗaukaka da girmar alʼummai a cikin birnin. 27Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.

Copyright information for HauSRK